Asabar 18 Yuli 2026 - 23:27
An Fara Gudanar da Tattakin Arba'in na Shekarar 1448 a Najeriya

Hauza/ Wasu daga cikin 'yan Shi'a kuma mabiyan Harkar Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), sun gudanar da tattakin Arba'in na Imam Husain (A.S) na farko a shekarar 1448 Hijira a yankin Birnin Kudu da ke jihar Jigawa.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, an gudanar da wannan tattaki ne a ranar Asabar, 3 ga watan Safar 1448 Hijira wanda yayi daidai da 18 ga watan Yulin 2026, tare da halartar dimbin masu juyayin Imam Husain (A.S) a yankin Birnin Kudu da ke jihar Jigawa a arewacin Najeriya.

An fara tattakin ne daga manyan wurare guda biyu. Hanya ta farko ta taso daga mikatin Babaldu, inda mahalarta daga garuruwa da ƙauyukan Sara, Samamiya, Tsangarwa, Kiyako, Babaldu, Budinga da sauran yankunan da ke kewaye suka haɗu zuwa cikin garin Birnin Kudu. Hanya ta biyu kuma ta tashi daga mikatin Tsamiya, tare da mahalarta daga Birnin Kudu, Iggi, Yalwan Damai, Kafin Gana, Kangire da sauran yankunan da ke makwabtaka.

Masu tattakin, waɗanda adadinsu ya kai dubunnai, sun sanya baƙaƙen kaya, suna ɗauke da tutoci da hotunan fitattun jagororin tafarkin gwagwarmaya, ciki har da Imam Khumaini (Q), Ayatullah al-Uzma Imam Khamene'i, Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei (DZ), Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da sauran shahidan gwagwarmaya. Sun gudanar da tattakin cikin waƙoƙin makoki da alhini domin tunawa da shahidan Karbala da kuma irin musibun da suka sami Ahlul Baiti (A.S) bayan yaƙin Ashura.

An kammala wannan tattaki cikin lumana da tsari, yayin da wasu daga cikin mazauna garuruwa da ƙauyukan da ke kan hanyar tattakin suka fito domin tarbar masu tattakin tare da nuna goyon baya da girmamawa gare su.

Tattakin Birnin Kudu shi ne tattakin Arba'in na farko da aka gudanar a Najeriya a shekarar 1448 Hijira. Ana sa ran sauran yankunan ƙasar za su gudanar da irin nasu tattakin a kwanaki masu zuwa, kafin a gudanar da tattakin rufe taron Arba'in na bana a babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha